Faransa ta ba ‘Yan tawayen Syria makamai
Faransa ta bai wa ‘yan tawayen kasar Syria makamai, domin tunkarar dakarun gwamnatin shugaba bashar Al Assad, da kuma mayakan jahadin da suka mamaye wasu yankuna a kasashen Iraqi da Syria.
Wallafawa ranar:
Shugaba Francois Hollande ya shaidawa manema labarai cewa sun aikawa ‘Yan tawayen da Makamai a watannin da suka gabata.
Shugaban yace matakin ya zama dole domin taimakawa mutanen Syria da ke son tabbatar da mulkin demokuradiya a kasar.
A cikin wata tattaunawa da Jaridar Le Monde, Hollande yace Faransa ta yi wa ‘Yan tawayen Syria guzurin makamai a bisa sharrudan muradun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu