Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Mayakan Iraqi sun kashe Ba’amurke a sakon Bidiyo

Kungiyar ‘Yan Tawayen Iraqi da ke fafutukar kafa Daular Islama a kasar sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka kashe wani Dan Jaridan Amurka James Foley da kuma barazanar kashe na biyu muddin Amurka ba ta dakatar da kai harin sama a kasar ba.

Hoton Bidiyon da Mayakan IS suka hallaka Dan Jarida  James Foley
Hoton Bidiyon da Mayakan IS suka hallaka Dan Jarida James Foley REUTERS/Social Media Website via REUTERS TV
Talla

Kungiyar ta nuna Dan Jarida na biyu Steven Sotloff inda ta ke cewar yanzu haka ransa na hannu shugaba Barack Obama.

Mahaifiyar Foley ta bayyaan shi a matsayin wanda ya bayar da ransa wajen tona asirin mayakan.

Fadar White House ta tabbatar da sahihancin Bidiyon. Kuma a cikin faifan Bidiyon an nuna Dan Jaridar yana karanta sako zuwa ga Amurka da iyalansa.

Bayan James ya kammala karanta sakonsa aka daba masa wuka a wuya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.