Isa ga babban shafi
Syria

An sake zargin Syria da yin amfani da makamai masu guba

Kasashen Amurka da Faransa sun sake zargi gwamnatin kasar Syria da yin amfani da makamai masu guba a wasu hare haren da dakarun kasar suka kai wa ‘yan tawaye, duk kuwa da cewa an kwashe kusan kashi 80 cikin dari na makaman masu guba, a karkashin yarjejeniyar da Rasha da Amurka suka amince.

Wasu mutanen Syria da suka shaki iska mai guda sakamakon harin makami mai guba da aka kai Kfar Zeita, a yankin Hama a kasar Syria.
Wasu mutanen Syria da suka shaki iska mai guda sakamakon harin makami mai guba da aka kai Kfar Zeita, a yankin Hama a kasar Syria. REUTERS/Stringer
Talla

Kakakin Fadagar White House Jay Carney yace suna da tabbacin gwamnatin Syria ta yi amfani da guba a hare haren da aka kai wa ‘Yan tawaye a cikin watan nan na Afrilu.

Wannan kuma ya biyo bayan zargin da gwamnatin Hollande na Faransa ta yi akan tana da wasu bayanan da suka nuna har yanzu gwamnatin Assad na amfani da makamai masu guba. Kodayake Faransa tace babu tabbas ga bayanan da ta samu.

Sai dai kuma kafar Telebijin din Gwamnati ta zargi kungiyar ‘Yan tawayen al Nusra wani reshen al Qaida da yin amfani da makaman masu guba a garin na Kafr Zita da ke cikin lardin Hama.

Yanzu haka dai ‘Yan tawaye da Gwamnati suna zargin juna ne da alhakin kai hare haren masu guba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.