Isa ga babban shafi
Chile

Jami'an agaji na kokarin kashe mummunar gobara a kasar Chile

Kawo yanzu dai wannan gobara da ta tashi tun ranar asabar da ta gabata, ta kona gidaje sama da dubu biyu tare da kashe akalla mutane 12 yayin da wasu mutanen kimanin dubu goma suka tsere suka bar Muhallinsu.

Gobara a Chile
Gobara a Chile REUTERS/Eliseo Fernandez
Talla

wannan gobarar dai ta fi karfi a yankunan da ke kusa da tsaunnuka na Jimenez da Mariposas da kuma Santa Elena Rocuant dake kewaye da ciyayi da kuma wasu gidaje na marasa galihu, yayin da iska ke neman kawo wa ma’aikatan agaji cikar a cikin ayyukansu.

shugaban kasar Mishell Bashelet ta kafa dokar hana shiga yankin domin bai wa jami’ai damar gudanar da aikin agaji da kuma tabbatar da tsaro.

hukumomi dai sun ce zasu yi kokarin shawo kan wannan gobara nan da kwanaki biyu zuwa uku kafin su iya kiyasta asarar da wannan gobarar ta haddasa

faruwar gobara a kasar ta chile ba sabon abu bane mussaman a lokacin rani, domin ko a shekarar 2013 gidaje 105 suka salwanta a Valparaiso inda lamarin ya shafi rayuwar mutane sama da dubu daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.