Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila ta kakabawa Falesdinawa sabbin takunkumi

Gwamnatin Isra’ila ta kakabawa Falesdinawa sabbin takunkumi da suka hada da kudaden haraji wannan kuma na zuwa ne bayan bangarorin biyu sun yi wata ganawa ta sasantawa tare da wakilin Amurka. Isra’ila ta rufe asusun kudaden harajin da ta karba a madadin Falesdinawa tare da dakatar da yarjejeniyar da ke tsakaninsu akan samar da cibiyar Gas a zirin Gaza.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Gali Tibbon
Talla

Tuni Babban wakilin Falesdinawa Saeb Erakat ya yi Allah waddai da matakin wanda ya kira ruba da ciki da kudaden Falesdinawa.

Wannan kuma na zuwa ne bayan wakilan Isra’ila da na Falasdinu, a jiya alhamis sun gana da manzon kasar Amurka na musamman Martin Indyk, domin ceto shirin samar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Shirin zaman lafiyar da kasar Amurka ke jagoranta, ya shiga hali na tangal-tangal a karshen watan Maris da ya gabata, bayan da Isra’ila ta ki cika alkawalin sakin wani adadi na fursunoni Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarinta, yayin da hukumar Falasdinawa ta mayar da martani ta hanyar rubutawa Majalisar Dinkin Duniya bukatar sanya shiga wasu yarjeniyoyin kasa da kasa.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry wanda ya yi rawa ya yi tsaki wajen ganin cewa wannan tattaunawa ba ta ruguje ba, a cikin makon jiya ya dora alhakin wannan sabon kiki-kaka akan wuyan Isra’ila.

Kafafen yada labaran gwamnatin Isra’ila sun ce an share tsawon akalla sa’o’I biyu ana wannan ganawa, amma babu karin bayani a game da muhimman batutuwan da taron ya cim ma matsaya a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.