Rasha
Rasha na binciken musabbabin hadarin jirgin saman da ya auku a kasar
Hukumomin Kasar Rasha sun fara bincike dan gano abinda ya yi sanadiyar hadarin wani jirgin fasinja da ya kashe mutane 44 da matukan sa guda shida a jiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun ma’aikatar agajin gaggawar kasar, ta ce jirgin kirar Boeing 737 ya tashi ne daga Moscow zuwa Kazan mai nisan kilomita 720 inda ya fadi lokacin saukar sa.
Rahotanni sun ce hadarin ya auku ne bayan jirgin ya yi yunkurin sauka a karo na biyu inda za a gudanar da bincike aka dalilin da ya sa ya kasa sauka a karon farko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu