Isa ga babban shafi
Syria-MDD

MDD za ta fara lalata makamai masu guba a kasar Siriya

Masana harkar nukiliya daga Majalisar Dinkin Duniya sun fara lalata makamai masu guba mallakar kasar Siriya, a karkashin yarjejeniyar Majalisar na ganin an raba kasar da makaman.Rahotanni daga Damascus sun ce, jiya masana dake karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya suka fara wannan aiki na lalata makaman da gwamnatin Syria ta gabatar musu.Ana saran masanan su lalata ton 1,000 na makaman dake dauke da sinadarin sarin da iskar gas, irin wanda ya halalka mutanen Aleppo, abinda ya janyo suka daga daukacin kasahsen duniya.Yayin da ake wanan aiki, shugaban Siriya Bashar al Assad, ya shaidawa wata jaridar kasar Jamus cewar, gwamnatin sa ta tafka kuskure a yakin da aka kwashe shekaru biyu ana fafatawa a kasar, sai dai ya musanta cewar dakarun sa sun yi anfani da makami mai guban kan fararen hula ranar 21 ga watan Agusta, matakin day a kaiga daukar kudirin Majalisar Dinkin Duniya wanda Russia da Syria suka jagoranta. 

Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria
Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria REUTERS/Khaled al-Hariri
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.