Isa ga babban shafi
Amurka-Masar-Jamus

Amurka da Jamus sun bukaci a sako Morsi

Gwamnatin Amurka da Jamus sun yi kira ga sojojin Masar su saki Mohammed Morsi da suka hambarar daga madafan iko, inda dubban magoya bayan shi ke ci gaba da zanga-zangar neman a mayar wa Morsi da mukamin shi na Shugaban kasa.

Wasu magoya bayan Morsi a birnin Alkahira
Wasu magoya bayan Morsi a birnin Alkahira REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Sabuwar gwamnatin rikon kwarya tace ana tsare da Morsi cikin matakan tsaro amma tun lokacin da sojoji suka tumbuke shi ba sake ganin shi ba.

Gwamnatin Amurka da Jamus sun bukaci sojojin kasar su gaggauta sakin shi domin kwantar da tanzoma a kasar.

Rahotanni daga birnin Alkahira da kuma sauran yankuna na kasar Masar na cewa a halin yanzu dai hankula sun kwanta, bayan da a ranar Juma’a dubban magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi suka gudanar da zanga-zangar neman a sake dawo da shi a kan karagar mulkin kasar.

Da farko dai an yi hasashen samun tashe tashen hankula bayan tasowa daga sallar Juma’a, saboda yadda masu adawa da Morsi suka bukaci masu irin nasu ra’ayi da su fito domin gudanar da zanga-zanga.

A nasa bangare kuwa Fira minsitan da aka nada bayan kifar da gwamnatin Morsi, Hazem Beblawi, har yanzu ya kasa kafa gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.