Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya dauki alwashin hukunta wadanda su ka kashe Jakadan Amurka

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya dauki alwashin tabbatar da an hukunta wadanda ke da hanu a cikin harin da ya yi sanadiyar kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar Jakadan kasar da wasu mutane uku Amurkawa. A cewar gwamnatin Amurkan harin ya iya yiwuwa an shirya shi ne tun farko.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Wannan kalamai na Obama sun zo ne a dai dai lokacin da kasar ta Amurka ta tura jiragen ruwan yakinta biyu zuwa mashigin ruwan kasar Libya.

Shugaban wanda yace harin ba zai bata dangantakar dake tsakanin Amurka da Libya ba, ya bayyana cewa hukunta wadanda suka aikata kisan ya zama wajibi.

“muna so mu aike da sako ga daukacin duniya cewar, duk wanda ke shirin mu da mugunta, to ya kwana da sanin cewar, babu aikin ta’adancin da zai dakushe fitilar muradun duniya, ko kuma girgiza muradun Amurka.” Inji shugaba Obama.

Jakadan Amurkan da aka kashe, Stevens, dan shekaru 52, ya kasance jakadan Amurka na farko da aka kashe a hari tun bayan kashe Jakadan kasar a Afghanistan Adolph Dubs, a shekarar 1979.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.