Isa ga babban shafi
Faransa-Syria

Faransa za ta amince da Gwamnatin ‘Yan tawayen Syria

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya nemi ‘Yan tawayen Syria kafa gwamnatin wuccin gadi don samun goyon bayan Faransa. Shugaban ya yi wani gargadi, idan gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kan ‘Yan tawaye, kasashen waje za su shiga tsakanin rikicin kasar.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Darren Staples
Talla

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya yi gargadin cewa, in har gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kan ‘yan adawan kasar, kasashen waje za su shiga a fafata da su a rikicin.

Shugaba Hollande yace dakarun kasashen waje suna ci gaba sa ido game da rikicin Syria, don hana amfani da makaman masu guba. Yana mai cewa Faransa za ta yi mu’amula da ‘Yan tawaye idan suka kafa Gwamnatin wuccin gadi.

Zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar Assad da aka fara tun a watan Maris din bara yanzu zanga-zangar ta rikide ya koma yakin basasa. ‘Yan rajin tabbatar da Demokradiyya sun ce akalla mutane sama da 20,000 aka kashe a rikicin

Manyan Kasashen Duniya duniya sun dade suna neman hanyoyin da zasu bi wajen kawo karshen rikicin Syria. Faransa da Amurka sun ce amfani da makamai masu guba zai bude hanyar da zata bas u damar shiga tsakanin rikicin kasar.

Sai dai Rasha da China sun dakile duk wata hanya da kakubawa kasar Syria takunkumi a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Tuni dai ‘Yan tawayen Syria suka ce za su koma neman taimakon daga Kungiyar Al Qaeda idan har kasashen Duniya suka juya masu baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.