Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Syria ta bude kofar tattaunawa game da ficewar Assad

Gwamnatin Syria tace a shirye ta ke ta tattauna game da ficewar shugaba Bashar al Assad daga karagar mulki domin kawo karshen jubar da jini a kasar da aka shafe fiye da shekara ana yi. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta gana da Rasha a Moscow.

Qadri Jamil, Mataimakin Firaministan kasar Syria wanda ya kai ziyara kasar Rasha.
Qadri Jamil, Mataimakin Firaministan kasar Syria wanda ya kai ziyara kasar Rasha. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

A jiya Talata an samu mutuwar a kalla kimanin mutane 198  da aka kashe sakamakon yaki da ake ci gaba da yi a yankin Aleppo tsakanin ‘Yan tawaye da dakarun Gwamnati.

A makon nan ne Mataimakin Firaministan Syria Qadri Jamil ya kai ziyara Rasha domin tattaunawa da mahukuntan kasar. Rahotanni sun ce Jamil ya kai ziyara Moscow ne domin tattauna hanyoyin da za’a shirya gudanar da zabe wanda zai ba kowa ‘Yancin tsayawa takara har da Bashar Assad.

‘Yan tawayen Syria sun ce sun fara nazarin samar da gwamnatin rikon kwarya amma babu wata alama da suka nuna ko gwamnatin za ta kunshi Jami’an Assad.

Tun fara rikicin Syria kasashen Yammci suka bukaci Assad yin bankwana da madafan iko bayan zargin shi da kashe mutanen shi a rikicin da aka kwashe tsawon watanni 17 ana yi tsakanin dakarun shi da ‘Yan tawaye.

Sai dai Duk wani yunkuri da kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin aiwatarwa akan Syria, China da Rasha sune kasashen da ke hawa kujerar na-ki.

‘Yan rajin tabbatar da demokradiya a kasar Sun ce sama da mutane 23,000 suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad a watan Maris. Amma Majalisar Dinkin Duniya tace mutane 17,000 ne suka mutu amma daruruwan mutane ne suka yi gudun hijira daga Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.