Ban Ki-moon yace akwai Sarkakiya da fargaba a ziyarar masu sa ido Syria
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran a gaggauta tura tawaggar sa ido don kawo karshen rikicin kasar Syrya, amma yace akwai sarkakiya da ban tsoro a ziyarar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mista Ban ya nemi hukumomin birnin Damascus su amince masu aikin agaji su shiga kasar, don bayar da tallafi ga daruruwan masu bukata, da ke cikin matsanancin hali sakamakon rikicin da aka kwashe shekara ana tsakanin Gwamnati da masu adawa.
A jiya alhamis Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasar Syria suka amince da yarjejeniyar ziyarar masu sa ido.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu