Isa ga babban shafi
Amirka-Afghanistan

Amirka Da Afghanistan Na Karfafa Zumunci

Kasar Amirka da kasar Afghanistan sun nanata burinsu na tabbatar da dorewar kyakkyawan dangantaka tsakanin su, koda bayan sojan Amirka sun janye daga kasar Afghanistan.Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai wanda yake cikin kwana na biyu da rangadin kwana hudu da yake yi a kasar Amirka, ya zauna tare da Sakatariyar Waje na Amirka Hilary Clinton domin shata yadda zumuncin nasu zai kara karfi nan gaba.Manyan jami'ai daga kasashen biyu sun fadi cewa tattaunawan ta shafi bunkasa harkokin aikin gona, yaki da safarar miyagun kwayoyi da horas da soja da ‘yan sandan kasar Afghanistan.Wannan ziyara na zuwa ne a wani lokaci da Shugaba Barack Obama ke ta tsara yadda Kasar Amirka zata  kara Dakaru 30,000 domin fafatawa da mayakan Taliban dake kasar Afghanistan.Hilary Clinton ta yaba da matakan da Shugaba Hamid Karzai ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa akasar.Ana saran Laraban nan Shugaba Hamid Karzai zai gana da Shugaba Barack Obama su tattauna cikin  sirri, sannan kuma daga bisani ya ci abincin dare tare da Mataimakin Shugaban kasar Amirka Joe Biden. 

La secretaire d'Etat américaine Hillary Clinton (D) participe à un diner avec le président Afghan Hamid Karzai (2è G) à Blair House. Washington, le 10 mai 2010.
La secretaire d'Etat américaine Hillary Clinton (D) participe à un diner avec le président Afghan Hamid Karzai (2è G) à Blair House. Washington, le 10 mai 2010. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.