Tsohon kwamandan Serbia, Janar Ratko Mladic, ya gurfana a gaban kotun Duniya a birnin Hague domin fuskantar zargi 11 na laifukan yaki da kisan kare dangi da keta hakkin bil’adama a yakin Bosnia a shekarar 1992-95.
Mai Gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifufuka, Luis Moreno Ocampo, ya nemi wani sabon sammacin kama shugaban ‘Yan Tawayen Congo, Janar Bosco Ntaganda, da Sylvester Mudacumura, wadanda suka jagoranci tawayen da aka kashe miliyoyin mutane a cikin shekaru 20 da suka gabata.
A wani Rahoton da Hukumar kare hakkin Dan adam ta Human Rights Watch ta fitar, rahoton yace a bara wani hari da kungiyar NATO ta kai ta sama ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 72 a Libya, tare da zargin kawance kasashen Turai da suka kaddamar da yakin kawar da Gaddafi.
Wasu manzannin diplomasiyar kasar Amruka guda 3 a yau juma’a sun gana da shugaban kasar Framsa mai jiran garo Francois Hollande a birnin Paris, kafin ziyarar da yake shirin kaiwa a kasar Amruka a moko mai zuwa, inda sabon shugaban na Fransa zai gana da shugaban kasar Amruka Barak Obama.
MASU kula da lafiya a kasar Amurka suna shawara kan yuwuwar fara amfani da wani magani mai suna Truvada, a matsayin wanda za a yi amfani da shi don rigakafin cutar HIV, maimakon bayar da shi don warkar da wadanda suka kamu da cutar AIDS.
Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama ya fito karara inda ya bayyana goyan bayan shi ga auren jinsi guda, a dai dai lokacin da Jahar North Carolina ta zama Jiha ta 30 da taki amincewa da auren.
A yau alhamis 10 ga watan Mai, rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin ta zama ranar Mata ta duniya, inda mata kan bayyana halin da suke ciki na matsi ko dadi, tare da ...
Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Syria, Kofi Annan, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewa, shirinsa na neman zaman lafiya shi ne mataki na karshe don kaucewa yakin basasa a kasar, a yayin da dakarun gwamati ke ci gaba da diran mikiya kan masu zanga zanga, da azabtar da fursunoni.
A ranar 6 ga watan Mayu ne Nicolas Sarkozy daya daga cikin aminan Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sha kaye a zaben Shugaban kasa bayan Faransawa sun juya masa baya inda suka zabi dan ...
A wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.
Shugabannin kasashen duniya da na Turai sun mika sakon taya murna ga Francois Hollande wanda ya lashe zaben shugaban kasar Faransa bayan ya kada Nicolas Sarkozy a zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu.
Gwamnatin kasar China tace Makaho dan rajin kare hakkin Bil’adama, Chen Guangcheng, zai iya neman izinin karatu a kasashen waje, a wani mataki na bude kofar kawo karshen sabanin da aka samu bayan ya tsere zuwa Ofishin jekadancin Amurka.
Shugaban Kasar China, Hu Jintao, ya bukaci Amurka da China mutunta mutuncin juna, sakamakon matsalar da aka samu na boye makaho mai kare hakkin Bil Adama, Chen Guangcheng, a Ofishin Jakadancin Amurka.
A rana irin ta yau ce dakarun Amurka suka ce sun kashe Osama bin Laden a Pakistan, amma kuma shugaban Amurka Barrack Obama ya yi kiran zama teburin sasantawa da Taliban a wata ziyarar bazata da ya ...
Kungiyoyin kwadago a kasashen Turai sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljuhun gwamnati domin gudanar da hutunsu na ma’aikata. Ma’aikata a Spain sun shiga zangar zangar ne saboda matsalar rashin aikin yi.
A YAU talata 1ga watan Mayu 2012 rana ce da Majalisar dinkin duniya ta kebe domin ma'aikatan kwadago a duniya, inda suke yin amfani da damar wajen bayyanawa mahukumtan kasashensu matsalolin da ...