Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra’ila ta haramtawa Falasdinawa yin cudanya da Yahudawa a Mota

Kasar Isra’ila ta haramtawa Falasdinawa yin cudanya da Yahudawa a cikin mota guda a yayin da suke kokarin zuwa wajen aiki ko dawo wa gida a gabar yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. Karkashin tsarin da Isra’ila ta kaddamar a yau Laraba, Falasdinawan da ke shiga Isra’ila da takardun shedar izini zuwa kwadago ba su da ‘yancin shiga mota guda da Yahudawa.

Falasdinawa na fuskantar kalubale a gabar yamma da kogin Jordan
Falasdinawa na fuskantar kalubale a gabar yamma da kogin Jordan
Talla

Ministan tsaron Isra’ila Moshe Yaalon ya ce wannan mataki ne na tsaro da zai ba su damar kula da Falasdinawan da ke shiga kasar ba tare da sun yi cudanya da Yahudawa ba.

Bayan daukar matakin, rahotanni sun ce ‘Yan sandan Isra’ila sun bindige wani Bafalasdine har lahira bayan ya abkawa ‘Yan sandan da Mota tare da raunana biyu daga cikinsu a birnin Kudus a yau Laraba.

Bayan kafa sabuwar gwamnati a Isra’ila, Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta nemi gwamnatin kasar ta gaggauta komawa kan teburin tattauna da Falastinawa da nufin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Manzon Majalisar a yankin Gabas ta tsakiya Nickolay Mladenov, ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar cewa, akwai gagarumin aiki a gaban kasashen duniya wajen ganin cewa an sake farfado da tattaunawa tsakanin Falasdinawa da Yahudawa bayan rugujewar tattaunawar a cikin watan Afrilun bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.