Afghanistan za ta gana da Taliban a Qatar
Wakilan gwamanatin kasar Afghanistan sun halarci kasar Qatar, inda za su tattauna har na tsawon kwanaki biyu da wakilan kungiyar Taliban
Wallafawa ranar:
Tattaunawar za ta gudana ne da nufin kawo karshen yakin Kasar da aka shafe tsawon loakci ana tafkawa.
Har ila yau, ganawar za ta samu halartar wakilai daga Kasar Pakistan kamar yadda mataimakin shugaban kwamitin samar da zaman lafiya ta Afghanistan, Abdul Hakim Mujahid ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.
Tun a shekara ta 2010 ne, tsohon shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya samar da kwamitin domin tattaunawa da kungiyar Taliban da sauran kungiyoyin dake tada kayar baya a Kasar, sai dai har yanzu ba a samu cikakkiyar nasara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu