Isa ga babban shafi
Indonesia

Indonesia na shirin zartar wa mutane 10 hukuncin kisa

Gwamnatin kasar Indonesia ta bada umarnin soma shirye shiryen aiwatar da kisan mutane 10 da aka zartarwa hukuncin kisa kan laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar, da suka hada da wani dan kasar Faransa Serge Atlaoui da ya haifar da takaddamar diflomasiya tsakanin Faransa da Indonesia.

Jami'an tsaron kasar Indonesia
Jami'an tsaron kasar Indonesia Reuters
Talla

Kakakin mai shigar da karar kasar ta Indonesia Tony Spontana ne ya sanar da AFP wannan bada umarnin, sai dai bai yi wani karin haske a kai ba.

Babu dai wata takamaimiyar rana da aka kebe da za a zartar da hukuncin kisan a kan mutanen 10 ‘yan asalin kasashen Australia da Faransa da Brazil da Philippines da Najeriya da Ghana da kuma Indonésia.

Mahukuntan Faransa na ci gaba da daga muryar neman ceto ran dan kasar ta su, a wajen madaukakiyar kotun kasar Indonesia bayan ta kara tabbatar da tabbatar da hukuncin kisan.

Serge Atlaoui, da aka daure a kurkukun kasar ta shekaru 10 da suka gabata, ya ce laifin da aka tuhume shi da aikatawa shi ne sakamakon gayyatarsa aikin hada injina a wata masana’anta da ya zaci ta gyaran duwatsu ma su daraja ne, amma kuma sai ta kasance inda ake sarrafa miyagun kwayoyi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.