Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta dakatar da hare hare ga mayakan Huthi a Yemen

Kasar Saudi Arabia ta sanar da kawo karshen hare haren da ta kaddamar kan Yan Tawayen Houthi dake kasar Yemen, bayan kwashe makwanni 4 tana jagorantar kai hari  

Dakarun Saudiya a Kasar Yemen
Dakarun Saudiya a Kasar Yemen RFI / Clarence Rodriguez
Talla

Mai Magana da yawun sojin kasar, Ahmed Al- Asiri yace, kawo yanzu sun kawar da duk wata barazanar dake zuwa daga ‘Yan Tawayen kan Saudi Arabia da makwaftanta.

Jami’in yace, zasu ci gaba da kawanya kan ‘Yan Tawayen ta mashigin ruwan kasar, yayin da ake sa ran mayar da hankali kan tattaunawar siyasa dan magnace rikicin kasar.

A nata bangaren, gwamnatin Kasar Amurka ta yi marhaba da kawo karshen hare haren tare da karfafa batun cewa ta hanyar tattaunawa ce za a shawo kan rikicin Yemen, yayin da tun a farko, Amurkan ta zargi Kasar Iran da taimakawa ‘Yan Tawayen Huthi da makamai domin ci gaba da tayar da kayar baya a Yemen da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Abdul-Rabuh Mansur Hadi.

Itama Kasar Iran ta yi marhaba da kudirin Saudiya na dakatar da hare haren, inda tace, hakan wani mataki ne na samar da maslahar siyasa a Kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.