Isa ga babban shafi
MDD-YEMEN

Jekadan MDD a Yemen ya yi Murabus

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen, ya bayyana ajiye mukaminsa bayan kokarinsa na sasanta rikicin kasar ya faskara. Wannan kuma wani mataki ne da ake ganin zai dagula kokarin da ake wajen sasanta rikici tsakanin ‘Yan tawaye da kuma dakarun kasar da ke samun goyon bayan Saudiya.

Jamal Benomar Jekadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen
Jamal Benomar Jekadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen DR
Talla

Sanarwar murabus din Jekadan na Majalisar Dinkin Duniya a Yemen na zuwa ne a yayin da kasar Saudiya da ke marawa sojojin kasar baya ke ci gaba da yin luguden wuta a akan ‘yan tawaye da Iran ke marawa baya.

Jekadan mai suna Jamal Benomar ya bayyana yin murabus bayan kokarinsa na sasanta rikicin kasar Yemen ya ci-tura, a yayin da ‘yan tawayen Huthi mabiya Shi’a suka karbe ikon fadar gwamnati tare da yi wa shugaban kasar daurin talala a gidansa a watan Janairu kafin ya tsere zuwa birnin Aden.

Jekadan dai ya ki samun goyon baya ne daga bangaren Saudiya da aminanta wadanda suka hadu suke kai wa ‘yan tawaye hare hare.

Saudiya da kawayenta na zargin jekadan ne da amincewa da bukatun ‘yan tawayen, yayin da kuma Iran ke zarginsu da rashin bin hanyoyin da suka dace domin shawo kan rikicin Yemen.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci ‘yan tawayen su fice daga Sanaa da dukkanin sauran wuraren da suka kwace bayan Saudiya ta kaddamar da hare hare a ranar 26 ga watan maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.