Isa ga babban shafi
Bangladesh

Bangladesh ta rataye Kamaruzzaman

Hukumomin Kasar Bangladesh sun rataye wani shugaban mabiya addinin Islaman kasar Mohammaed Kamaruzzaman saboda samunsa da laifin jagorantar kashe mutanen da aka yi a shekarar 1971 zamanin yakin neman ‘yancin kan kasar daga Pakistan.

Jami'an Tsaro tare da Mohammad Kamaruzzaman da aka zartar wa hukuncin rataya a Bangladesh
Jami'an Tsaro tare da Mohammad Kamaruzzaman da aka zartar wa hukuncin rataya a Bangladesh AFP/MUNIR UZ ZAMAN
Talla

Ministan sharia Anisul Huq yace an rataye malamin ne a cikin daren jiya Assabar.

Kamaruzzaman shi ne Mutum na uku daga cikin shugabannin Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ta Jama’atul Islami da aka samu da laifin kisan dubban masu ra’ayin Pakistan.

Jam’iyyar Jama’at ta la’anci hukuncin da aka yanke wa malamin na addini tare da yin kira ga magoya bayanta su fito zanga-zanga da za ta jagoranta a ranar Litinin.

Mahukuntan Bangladesh dai sun zartar da hukuncin ne duk da kiranye kiranyen da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama suka yi na a dakatar da zartar da hukuncin saboda ya sabawa dokokin duniya.

A watan Disemban 2013 an zarwarwa Abdul Quader Molla, irin wannan hukuncin wanda shi ne shugaban Jam’iyyar Jamaat a Bangladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.