Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

An shiga matakin karshe a yarjejeniyar Nukiliyan kasar Iran

Jiya Lahadi aka shiga mataki na karshe na mawuyaciyar tattaunawar da ake yi akan shirin nukliyar kasar Iran, inda ake ganin yiyuwar cimma yarjejeniya tsakanin kasar ta Iran da gungun manyan kasashen duniya 5 da dadin 1. Ana taron ne da zummar ganin an cimma yarjejeniya kafin cikar wa’adin da aka gindaya na gobe Talata, game da shirin Nukiliyan kasar ta Iran.Yayin da ya rage sa’oi kalilan wa'adin yarjejeniyar ya cika, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace shi da takwaran shi na Iran Mohd Javad Zarif, suna aiki tare kuma al’amurra na tafiya daidai duk da cewa akwai wasu kurakurai da ake kokarin magancewa. Shugaba Hassan Rouhani yace Iran ta bada duk wani hadin kai da ake bukata a yarjejeniyar, inda ya kara da cewa yanzu ya rage ga kasashen yamma su tabbatar da alkawarin da suka dauka ganin tsawon lokacin da aka dauka ana kokarin kawo karshen sa-in-sa da aka kwashe shekaru goma sha biyu tsakanin Iran da kasashen. Ana sa ran yarjejeniyar zata mayar da hankali kan turasasawa Iran ta bayar da hadin kai ga masu bincike, a ziyarar da suke shirin kaiwa a cibiyar makamashin Nukiliyan nata, a duk lokacin da aka bukata Tuni dai Fraiministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai hatsari, muddun aka cimma yarjejeniyar a cewarsa hakan zai baiwa Iran damar zama mai karfin fada aji, tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya. 

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaran shi na Iran Mohammad Javad Zarif
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaran shi na Iran Mohammad Javad Zarif Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.