Isa ga babban shafi
Yemen

Harin Yemen ya kashe mutane 15 a Sansanin 'Yan gudun hijira

Wani harin sama da aka kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira na yankin Arewacin Yemen, ya hallaka mutane 15, yayin da majiyar  jami’an tsaro, ta tabbatar cewa Jiragen yakin gamayyar Dakarun kungiyar kasashen Larabawa ne, suka kaddamar da harin a yankin da ‘yan tawaye ke ci gaba da rikewa  

Fashewar wasu Bama-bamai a Yemen
Fashewar wasu Bama-bamai a Yemen REUTERS/Nabeel Quaiti TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Kungiyar nan ta Likitocin da basu da iyaka na Majalisar dunkin Duniya, Medicine Sans Frontiers wacce asalinta daga kasar Faransa ne, ta tabbatar cewa, an dauki Gawawwaki 15 da wasu mutane 30 da suka jikkata,  inda aka kai su  wata cibiyar kiyon lafiya da ke kusa da Sansanin Al-Mazrak na Lardin Hajja.

Kungiyar ta ce tabbas harin Jiraghen sama ne, kuma akwai yiyuwar samun karuwar mamata a wannan harin.

Kungiyar ta kara da cewa, hatta sansanin ‘yan gudun hijirar da ke wurin harin ya shafa.

Wasu Rahotanni na cewar gamayyar Dakarun kassahen Larabawan, sun lashi takobin ci gaba da kai hare-haren har sai Dakarun da ke samun goyon bayan kasar Iran sun yi saranda.

Wannan dai shi ne karo na 5 da aka ce Dakarun na Larabawa, sun kaddamar da irin wannan harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.