Isa ga babban shafi
Tunisia

Za a yi gangamin yaki da ta'addanci a Tunisia

Hukumomin kasar Tunisia sun shirya gudanar da wani gangami, don nuna adawa da ayyukan ta’adanci a cikin kasar. Ana sa ran shugaban Faransa Francois Hollande zai hallici gangamin da ya biyo bayan mumunan harin ta’adancin da aka kai a gidan tarihin kasar, lamarin da ya hallaka mutane 23Dubban al’ummar kasar ake sa ran zasu fito a matsayin tsintsiya madaurin ki daya domin yin adawa da ayyukan ta’adancin.Shugaba kasar Tunisia Beji Kaid Essebsi ya yi kira ga al’ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu, a abun da ya kira gangamin yaki da ayyukan ta’adanci. Za’a gudanar da gangamin a ranar da ake sake bude gidan tarihin da ‘yan ta’adan suka kai harin da ya hallaka mutane 21, yawancinsu masu yawon bude ido daga nahiyar Turai. Shugabam Francois Hollande na daga cikin shugabanin wasu kasashen duniya da ake sa ran zasu halarci gangamin. Kungiyar ISIL mai da’awar kafa daular Islama ta dauki alhakin kai harin da ya matukar girgiza al’ummar kasar ta Tunisia dama sauran duniya baki daya.  

Shugaban kasar Tunisia Beji Caïd Essebsi
Shugaban kasar Tunisia Beji Caïd Essebsi REUTERS/Zoubeir Souissi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.