Isa ga babban shafi
Yemen

Mutane 61 sun mutu cikin kwanaki 3 da aka shafe a rikici a Yemen

Akalla mutane 61 ne suka mutu a cikin kwanaki 3 da aka kwashe ana tafka fada tsakanin ‘yan tawayen Shi’a da wasu Dakaru masu biyayya ga hukumomin kasar Yemen, a yankin kudancin Aden.Wata majiyar asibiti ta tabbatar da mutuwar mutanen da suka samu munanan raunuka.Babban Daraktan wata Cibiyar kiyon lafiya ta birnin Aden Al-khader Lassour ya shaidawa Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar akalla mutane 203 ne suka jikkata, bayan mutuwar wasu mutanen 61.Al’amurra dai sun kara tsauri a birnin Aden, a yayin da dakarun kasar Saudi Arebiya ke jagorantar farmakin da ake ci gaba da kai wa ‘yan tawayen na Huthi da yanzu haka ke rike da wasu sassan birnin na Aden.Wata kafar Tallabijin ta cikin gida ta tabbatar da ganin dakarun kasar ta Saudi Arebiya, na kwasar jami’an diplomasiyya ‘yan kasashen waje daga Aden, sai kalilan kamin Dakarun na Saudiyya su kaddamar da hari a can.Duk wannan kuma na zuwa ne a yayin da ake sa ran taron kasashen Larabawa ya goyi bayan matakin da Rundunar Sojin Saudi Arebiya ta dauka na kai hari ga ‘yan tawayen na Huthi.Taron na kasashen Larabawa kuma zai samu halartar shugaban kasar ta Yemen Abedrabbo Mansour Hadi, da Sarki Salman na Makka da kuma Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ban Ki moon. 

Dakarun kasar Yemen suna sintiri a birnin Aden
Dakarun kasar Yemen suna sintiri a birnin Aden REUTERS/Nabeel Quaiti
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.