Isa ga babban shafi
Yemen

Ana ci gaba da yi wa ‘Yan tawayen Huthi luguden wuta

Sojojin kawance karkashin jagorancin kasar Saudiyya suna ci gaba da kai farmaki akan sansanonin ‘yan tawayen kungiyar Huthi da ke rike da muhimman yankunan kasar Yemen, yayin da kasar Amurka ta bayyana cewa za ta taimaka wa sojojin kawancen a fannoni da dama domin samun nasara a wannan farmaki.

REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Jiragen saman yakin kasar Saudiyya sun share tsawon yinin jiya suna kai farmaki akan ‘yan tawayen na Huthi, lamarin da kuma kasar Iran da ke mara wa ‘yan tawayen baya ta bayyana shi da cewa zai iya haifar da mummunan rikici a yankin baki daya.

Jagoran ‘yan tawayen Abdulmalik Al-Huthi, wanda ke gabatar da jawabi a wata kafar talabijin ta kasar, ya bukaci magoya bayansa da su nuna turjiya dangane da wannan farmaki da dakarun kasashen ketare ke kai ma su.

A wani taron gaggawa da suka gudanar a birnin Al kahira na kasar Masar, manyan hafasoshin sojan kasashen da ke da hannu a farmakin, sun ce ba za a dakatar da kai hare-hare ta sama ba sai zuwa lokacin da aka cim ma manufar kaddamar da su.

A wata sanarwa da ta fitar, kasar Amurka ta ce za ta taimaka wa kasashen da ke kai farmakin ta fannoni da dama, da suka hada da shayar da jiragen yakinsu mai a sama, da kuma sauran fasahohi da bayanai ta hanyoyin sadarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.