Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta yi wa manyan kasashen Duniya kememe

Kasar Iran ta ce ko kusa bata amincewa abinda ta kira kisisinar kasashen yammacin Duniya ba wajen hanata ci gaba da sarrafa Uranium mai samar da Makamashin Nukiliya da ka iya sarrafawa a samu Makaman kare dangi

Talla

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya amincewa matsayin da wakilan kasar tasa suka tsaya kyam akai, na kin amincewa da tayin da kassahen Duniyar suka yi masu.

Yanzu haka dai kwanaki 10 kacal ne suka rage a kammala batun tattaunawar da ake tsakanin Iran da manyan kassahen Duniya da suka hada da Amurka da faransa da Rasha da Jamus da China.

Kassahen dai na zairin Iran ne da kokarin mallakar Makaman kare-dangi ne, abinda suke kallo a matsayin babbar barazana gaabokiyar kawancensu wato Isra’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.