Isa ga babban shafi
Iraqi

IS ta tarwatsa gidan tarihin Mosul

Mayakan kungiyar IS sun kai hari akan wani gidan tarihi tare da lalata abubuwan da ke ciki, kamar yadda suka nuna a wani hoton Bidiyo da suka fitar. IS ta tarwatsa Gumaka a hoton bidiyon da kungiyar ta fitar tare da nuna yadda mayakan suka dirran ma gidan inda suka yi amfani da wasu makamai suna lalata kayyayakin da suka danganta ajiye su da bautar gumaka

Mutane sun taru a inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul
Mutane sun taru a inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul REUTERS/Stringer
Talla

Wani daga cikin mayakan da ya boye fuskarsa a hoton bidiyon ya ce Manzon Allah ya bayar da umarnin lalata gumaka a duk lokacin da aka sami nasarar yaki a kowace kasa.

Wani ma’aikacin gidan tarihin da aka kai harin ya ce yawancin gumakan da ISI ta lalata na daga cikin wadanda aka kwaso ne daga garin Mosul bayan mayakan sun kwace ikon garin a watan Yunin da ya gabata.

Kungiyar IS mai da’awar kafa daular Islama a gabas ta Tsakiya a baya ma ta kai munanan hare hare a cikin kasar ta Iraqi tare da lalata wurarren ibadun yan shi’a da muja’miar Kiristoci da ke karkashin ikon su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.