Isa ga babban shafi
Syria

Kungiyar IS ta sace Mutane 90 a Syria.

Mayakan kungiyar IS sun sace mabiya addinin Kirista 90, bayan farmakin da suka kai a wasu kauyuka dake arewa maso gabashin kasar Syria

Mayakan IS a Syria.
Mayakan IS a Syria. © AP
Talla

Wata Kungiyar kare hakkin dan Adam ce, ta bayyana haka yayinda, a karo na farko kenan da mayakan IS suka yi awan gaba da tarin mabiya addinin Kirista a lokaci daya, duk da cewa a baya, sun yi garkuwa da dubban mutane, a yayinda suke cigaba da ayyukan ta’addanci a Iraqi da Syria.

Sai dai kungiyar dake kare hakkin adam din, bata tabbatar ko akwai kananan yara da mata ba, cikin mutanen da IS ta sace kuma bata san inda aka boye su ba.

Sace mutanen na zuwa ne, bayan ‘yan kungiyar ta IS, sun yi nasarar karbe garuruwan Tal Shamiram da Tal Hermuz, da ke karkashin ikon mayakan Kurdawa, a wani dauki ba dadi da ya kaure tsakaninn bangarorin biyu ranar litinin.

Kuma IS ta kai farmakin ne, a matsayin martani ga Mayakan Kurdawa da suka kai musu hari a makon daya gabata tare da taimakon kasashen da suka yi kawance da Amurika wajan yan kungiyar IS.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.