Isa ga babban shafi
Japan

kungiyar Isis ta halaka dan kasar Japan na biyu

Mayaka yan kungiyar Isis sun halaka dan kasar Japan  da suke garkuwa da shi, kamar dai yada hukumomin kasar suka sanar.Gwamnatin Japan cikin kaduwa da baki cikin ta bayana cewa ba gudu ba ja da baya a kokari da take na baiwa wasu kasashe taimako na yaki da ta’adanci a Duniya. 

Firaministan Japan  Sinzo Abe
Firaministan Japan Sinzo Abe Reuters/路透社
Talla

Firaministan kasar Japan Sinzo Abbe ya nuna cewa wanan kisa na bayyana matukar rashin girmama dan adam daga mayakan Isis kuma Japan zata ciggaba da bayar da goyan baya domin kawo karshen wanan kungiya ta yan ta’ada.

Amaruka ,Faransa, Birtaniya, Shugabanin wadanan kasashe sunyi tir da allah wadai da wanan ta’asa da yan kungiyar Isis suka aikata.
Obama wanda a wata sanarwa da ta futo daga fadar White House ya bayyana alhini sa dama juyayi da kuma tabbatar da cikkaken goyan bayan Amaruka wajen yaki da ta’adanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.