Isa ga babban shafi
Yemen

Majalisar Yemen ta ki amincewa da marabus din shugaban kasar

Kasar Yemen ta kara fadawa cikin rudani bayan da shugaban kasar Abdurabuh Mansur Hadi ya yi marabus daga mukaminsa sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin kasar ta yi marabus.

Shugaban Yemen Abdurabuh Mansur Hadi
Shugaban Yemen Abdurabuh Mansur Hadi REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

A wasikarsa ta marabus, shugaba Hadi ya ce ba zai iya ci gaba da tafiyar da mulkin kasar ba, to sai dai kawo yanzu Majalisar Dokokin kasar ta ki amincewa da marabus din shugaban.

Kasar Yemen dai na fama da rikici ne sakamakon yadda ‘yan tawayen Huthi suka kwace iko da muhimman wurare a birnin Sana’a fadar gwamnati, yayin da ‘Yan Huthin wadanda mabiya mazhabar Shi’a ne ke kara wanzar da ikonsu a wasu yankunan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.