Isa ga babban shafi
ICC

An bukaci ICC ta gurfanar da kasar Korea ta kudu

Babban zauren mashawarta na majalisar dinkin duniya ya yi kira da a mika gwamnatin Korea ta kudu ga kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, domin ta fuskanci tuhumar laifin cin zarafin bil’adama

en.wikipedia.org
Talla

Zauren majalisar dinkin duniyar ta yanke wannan kudirin ne a jiya alhamis, bayan kasashe 116 cikin 193 sun nuna amincewarsu da hakan, ta hanyan kada kuri’u a zauren majalisar .

Kudirin ya nemi kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyan da ya kai kasar Korea ta kudu kotun hukunta manyan laifuka ta ICC kuma kwamitin ya amince da takunkuman da take shirin kakabawa kasar a sakamakon laifin zaluntan yan kasar ta hanyar dakile su daga samun cikakken yancin sun a yan adam.

Tun a watan nuwamba ne, majalisar ta fara kada kuri’u akan wannan batun, inda kasashe 111 suka amince a wannan lokacin yayinda kasahe 19 suka ki amincewa baya ga sauaren kasashen 55 suka janye daga kada kuri’un.

Sai dai a dayan bangaren kuwa, ba lalle bane, kwamitin tsaron yayi aiki da kudirin majalisar dinkin duniyan, yayinda ya ake sa ran ranar litinin mai zuwa, kwamitin zai gana da Kasar Korea ta kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.