Isa ga babban shafi
Pakistan

Ana zaman makoki a Pakistan

Kasar Pakistan ta fara zaman makoki na kwanaki uku kan gisan gillar da kungiyar Taliban ta yi wa mutane 141 a makarantar ‘yayan sojojin da ke Peshawar inda ta kashe dalibai 132.

Iyayen yaran da Taliban ta kashe a Pakistan suna cikin juyayi.
Iyayen yaran da Taliban ta kashe a Pakistan suna cikin juyayi. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Yanzu dai haka ‘yan uwa da iyayen yaran da aka kashe a harin na garin Peshawar sun fara shirin jana’izarsu inda aka sanya gawawwakin a cikin akwatuna kuma aka jera firanni akansu.

Firaministan kasar Nawaz Sharif wanda nan take ya bar Islamabad zuwa inda aka kai harin a jiya Talata ya bayyana zaman makoki na kwanaki uku bayan ya yi Allah wadai da harin.

Sharif ya bayyana cewar babu yadda zai zauna a Islamabad lokacin da ake kashe daliban da ya bayyanasu a matsayin ‘ya’yansa, inda ya jagoranci taron majalisarsa a Peshawar don nazarin matakan da gwamnatin kasar za ta dauka.

Tuni shugabanin kasashen duniya da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon suka yi Allah wadai da harin.

Mayakan na Taliban sun kai mummunan harin ne a jiya Talata kuma wadanda al’amarin ya faru a gaban idon su sun ce bayan mayakan sun jefa bom sun kuma bi aji aji na daliban makarantar suna bindige yara.

Firaminsitan Pakistan yace wannan mummunan al’amari ne da ya shafi daukacin al’ummar kasar.

Malala Yousafzai, da ke da’awar tabbatar da ilimin ‘ya’ya mata a Pakistan kuma wacce ta karbi kyautar Novel ta la’aci harin tare da bayyana bakin cikinta.

An danganta al’amarin a matsatin mafi muni daga cikin hare haren da Taliban ta kai a Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.