“Goyon bayan Falasdinawa illa ne ga Isra’ila”
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi koken cewar goyan bayan da kasashen Turai ke bai wa Falasdinawa kan shirin Majalisar dinkin Duniya na tilasta ma ta ficewa daga yankunan da ta ke mamaye da su illa ne ga Isra’ila. Netanyahu yace duk wani yunkuri makamancin haka zai haifar da tabarbarewar al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Isra’ila, saboda haka ba za su amince da shi ba.
Wallafawa ranar:
Birtaniya da Sweden da Faransa da Spain sun amince a ba Falasdinawa 'Yanci. Amma Isra’ila ta yi watsi da matakin tana mai cewa zai kara lalata yunkurin komawa teburin tattaunawar sasanta rikicin gabas ta tsakiya.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Netanyahu da John Kerry sun yi wata duguwar ganawa kan tsaron kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu