Isa ga babban shafi

An sami girgizar kasa a Japan

Yau Lahdai jami’an gwamnatin kasar Japan sun ce wata girgizar kasar mai karfin maki 6 da digo 2, tayi sanadiyyar raunata kusan mutane 40, 7 daga cikinsu suna cikin mummunan hali.Girgizar, daka ce tafi yin ta’adi a yankunan dake da tsauka, ta kuma lalata gidaje da hanyoyin yankin Nagano, dake arewa maso yammacin birnin Tokyo, inda wani gidan talibijin ya nuno wasu gidaje sun rushe gaba daya.Hukumar bincike kan yanayi tayi gargadin yuwuwar samun karin girgizar sakamakon wannan, nan da mako mai zuwa. 

Wani yankin da aka yi girgizar kasa a Japan a baya
Wani yankin da aka yi girgizar kasa a Japan a baya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.