Isa ga babban shafi
Afghanistan

Fyade: An daure Malamin addini a Afghanistan

Wata kotu a kasar Afghanistan ta yanke wa wani Malamin addinin musulunci hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan samunsa da laifin yi wa wata yarinya Dalibarsa ‘yar shekaru 11 fyade. Yarinyar ce ta shigar da kara a kotu duk da iyayenta sun la’anci bacin sunan da ta kawo wa gidansu. Kuma Kotun ta yanke hukuncin ne a jiya Assabar a birnin Kabul.

Wata Yarinya kwance a gadon Asibiti da ake kula da lafiyarta a birnin Kabul
Wata Yarinya kwance a gadon Asibiti da ake kula da lafiyarta a birnin Kabul AFP Photo / Shah Marai
Talla

A watan Maris ne Malamin mai suna Muhammed Amunullah Barez da ke karantar da ‘ya'ya mata karatun Islama ya yi wa yarinyar fyade mai suna Hasina Sarwari.

Da farko yarinyar ta nemi boye al’amarin da ya faru, amma daga baya jini ya fara zuba da har ya kai ta kwanta Asibiti, lamarin da ya sa likitoci suka gano fyade ne aka yi ma ta.

Iyayen yarinyar sun so kashe ta saboda bacin sunan da ta kawo wa gidansu, amma ‘yan rajin kare mata suka cece ta.

Malamin dai ya amsa laifin aikata fyaden, amma ya shaidawa kotu cewa da amincewar yarinyar ya kwanta da ita.

Daga karshe dai Kotun ta yi watsi da hujjojin Malamin da ya gabatar, domin zai iya sa ya kaucewa hukuncin dauri don a yi masa bulala da shi da yarinyar tare da daukarta a matsayin mazinaciya maimakon la’akari da fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.