Isa ga babban shafi
Hong Kong

An fara tattaunawa da masu zanga zangar Hong Kong

Hukumomin birnin Hong Kong suka hau teburin sasantawa, da masu zanga zangar neman ganin an tabbatar da tsarin democradiyyar a yankin. Ana sa rai tattaunawa ta yau Talata zata kawo karshen gangamin da aka shafe makonnin ana yi a kan titunan birnin, lamarin da kawo tsaiko a harkokin yau da kullunm.Wannan na zuwa ne sa’oi kadan baya Shugaban yankin Hong Kong Leung Chun-ying, yace zaben da za a gudanar zai baiwa talakawa damar shiga a dama dasu a harkokin siyasa yankin.Cikin wata hira da yayi da kafafen yada labarum kasashen waje, Chun-ying, dake ci gaba da fuskantar matsin lamba, ya sake jaddada matsayin shi kan zai yi wuya a sami gudanar da tsaftataccen zabe a yankin. Yau fiye makonni 3 kenan, da masu zanga zangar suka rurrufe manyan titunan birnin na Hong Kong dake kudancin kasar China, inda suke neman a inganta tsarin democradiyya a yankin.Zanga zangar na da nasaba da karuwar rashin daidaito tsakanin al’umma, da kuma tsadar rayuwa da jama’a ke kara shiga.Duk da cewa zanga zanga na gudana cikin lumana, sai dai kuma an samu tashe tashen hankula a wasu wuraren, lokacin da ‘yan sanda suka yi yunkurin bude hanyoyin da aka rurrufe.Wannan kuma na matsayin daya daga cikin kalu bale mafi girma da hulumomin birnin Beijing ke fuskanta, tun bayan gangamin neman tabbatar da tsarin democradiyya, da aka yi cikin shekarar1989 a dandalin Tiananmen. 

Masu zanga zanga tare da 'yan sanda a Hong Kong
Masu zanga zanga tare da 'yan sanda a Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.