Isa ga babban shafi
Myanmar

Kasar Myanmar ta saki Fursunoni sama da dubu 3, ciki kuwa hadda Jami’an Soji

Gwamnatin kasar Myanmar ta saki Fursunonin siyasa fiye da dubu uku, a matsayin afuwa ga fursunonin kamar yanda hukumomin kasar suka sanar. Daga cikin wadanda aka yi wa afuwar kuwa hadda sojoji da kuma ‘yan siyasa

hurriyetdailynews.com
Talla

Daruruwar fursunoni da ke tsare a gidajen yarin Myanmar ne suka fara samun afuwa, cikinsu kuwa har da yan siyasa da tsofafin sojoji, kuma hakan na a matsayin shirin jinkai da sabon shugabanci kasar ke aiwatarwa.

Wannan afuwar dai ta zo ne a daidai lokacin da kasar ke shirin karbar taron shugabanin kasashen Duniya a watan Nuwamba mai zuwa, kuma dai daga cikin jerin sauye-sauyen da kasar kan aiwatarwa tun bayan kawo karshan mulkin kama-karya na shekarar 2011.

A labarin da Ministan yadda labarai na kasar Ye Htut ya fitar a shafinsa na facebook ya ce shugaba Thein Sein ya yi wa mutane sama da dubu uku afuwa, wadanda suka hada da ‘yan asalin kasashen waje 58, inda ya ce haka na a matsayin jinkai sannan kuma zai kawo zaman lafiya a kasar.

Kafin wadannan sauye sauye da hukumar kasar ta Myanmar ke kan aiwatarwa, a can baya kungiyoyi kare hakkin bil’adama sun zargi gwamnati da tsare fursunonin siyasa sama da dubu biyu a gidajen yarin kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.