Isa ga babban shafi
Hong Kong

Zanga-zangar Hong Kong ta kara girma bayan cika Dare na 3

Dubban masu zanga-zangar rajin kare Dimokradiyya a Hong Kong sun kara kaimi tare da yin amfani da zanga-zangar domin cika shekaru 65 da mulkin Kwamunisancin kasar China, inda ake sa ran kara fitowar mutane masu halartar zanga-zangar

rfi
Talla

Masu zanga-zangar dai na rike ne da wasu Fitillu masu dan karan haske, abin da ke alamta samun nasara da suke nuna cewar sun samu, a dayan bangaren kuma da rera wake-waken cikar shekaru 65 da mulkin kwamunisanci.

A yayin da aka kammala Dare na 3 da soma ita wannan zanga-zangar masu tsokaci kan harkokin diplomasiyya na Duniya, da kuma ‘yan Siyasar Hong Kong na ganin cewar abu mafi kyau dai shi ne shugaban ya yada kwallon Mangoro hakan, ya huta da Kuda.

Ko a wurin zanga-zangar ma al’ummar Hong Kong na bayyana kasawar shugaban na fuskantar masu zanga-zangar saboda yanda matsalar ta yi kamari.

Kusan ko’ina a Hong Kong dai ana jin harshen masu zanga-zangar da suka tada Tutar kasar China a dandalin Bauhinia da ke a tsakkiyar garin Wanchai, a yayin da Jirage masu saukar Ungulu ke shawagi ta sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.