Isa ga babban shafi
IS-Amurka

Wasu kasashen Larabawa sun bi Amurka a yaki da Kungiyar ISIS

Wasu Kasashen larabawa sun shiga cikin jerin kasashen yammaciN Duniya da Amurka wajen kai hare-hare a kan mayakan jahadin kasashen Iraqi da Siriya na kungiyar ISIS bisa jagorancin kasar Amurka

morningflash.com
Talla

Kasashen na larabawan yankin gabas ta tsakkiya da suka shiga cikin jerin kasashen rundunar hadakar da Amurka ke jagoranta, wajen kokarin kawar da kungiyar ISIS ta mujahidan da suka bayyana kansu a matsayin masu fafutukar kafa Daular su a yankin gabas ta tsakkiya, sun hada ne da Jordan da saudiyya da Qatar da Bahrain da kuma kasar Hadaddiyar Daular laraba, wadanda a ranar talatar da ta gabata suka bi sahun kasar Amurka wajen kai hare-hare ta sama da Amurka ta jagoranta.

A jiya laraba ne kasar Amurka ta tabbatar da kai hare-haren ta sama da kasar ta Jordan ta kai kan mayakan na cikin kasar Siriya.

Harin da Jordan ta kai a cikin Daren jiya laraba, ya biyo bayan wasu sababbin hare-hare guda 5 ne, da kasar Amurka ta kai kan ‘yan kungiyar ta ISIS a kasashen Iraqi da Siriya, a kwana na 2 na kaddamar da yakin.

A ranar talatar da ta gabata ne dai kasar ta Jodan ta tabbatar da aniyarta ta kasancewa a cikin jerin kasashen da za su yaki kungiyar ta ISIS a kasashen Iraki da Siriya domin kawo karshen zaman zullumin da suka haddasawa yankin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.