Isa ga babban shafi
Syria-Iraq-MDD

Dubban Kurdawa sun bar gidajensu a kasar Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin sa’o’I 24 da suka gabata, Kurdawan Syria akalla dubu 70 ne suka bar gidajensu sakamakon barazanar da suke fuskanta daga mayakan jihadi na kasar.  

Mutanen Syria da ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Lebanon
Mutanen Syria da ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Lebanon REUTERS/Hassan Abdallah
Talla

Yanzu haka dai daruruwan dakarun kungiyar ta mayakan jihadi ne suka yi wa garin Ain Al-Arab wanda mafi yawan mazaunansa Kurdawa ne kawanya, yayin da a hannu daya ake ci gaba da gwabza fada tsakanin masu da’awar jihadin da kuma mayakan sa-kai na kurdawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin bai wa fararen hular yankin kariya daga mayakan wannan kungiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.