Isa ga babban shafi
Iraq

Kasashen Turai 7 zasu ba Kurdawan Iraqi makamai

Sakataren Harakokin tsaron Amurka, Chuck Hagel yace yanzu haka kasashen Turai bakwai ne suka bayyana aniyarsu na bai wa Kurdawan Iraqi makamai domin kare kansu daga mayakan ISIS. Hagel ya bayyana kasashen da suka hada da Albania da Canada da Croatia da Denmark da Italiya da Faransa da Britaniya.

Dakarun Kurduawa da ke yaki da Mayakan IS cikin motarsu a  Jalawla, lardin Diyala.
Dakarun Kurduawa da ke yaki da Mayakan IS cikin motarsu a Jalawla, lardin Diyala. Reuters
Talla

Kasar Iran dai ita ce kasa ta farko da ta fara bai wa Kurdawan makamai.

Tuni kuma kasashen Albania da Birtaniya suka fara shigar da kayyaki zuwa Iraqi.

Tun a ranar 8 ga watan Agusta ne Amurka ta kaddamar da farmaki akan Mayakan Is da suka kwace ikon yankin arewacin Iraqi, bayan kuma sun bayyana kafa sabuwar daular Musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.