Isa ga babban shafi
Isra'ila-Syria

An harba makaman roka daga Syria zuwa Golan

Yayin da aka shiga rana ta 48, a yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da kungiyar palasdinawa ta Hamas, yau Lahadi wasu makaman rokan da aka harba daga kasar Syria, sun fada a yankunan tiddan Golan, da Isra’ila ta mamaye. Mai magana da yawun rundunar sojan kasar ta Yauhudu tace, a kalla makaman roka 5 ne suka sauka a wurare daban daban a tiddan na Golan, sai dai sojojin basu mayar da martani ba.Ko a cikin watan daya gabata, wasu makaman rokan da aka harba kasar Isra’ila daga Syria, sun janyo martani kan wuraren da ke hannun sojan na Syria. 

Wasu sojan kasar Isra'ila suna kallon kasar Syria, daga tiddan Golan
Wasu sojan kasar Isra'ila suna kallon kasar Syria, daga tiddan Golan REUTERS/Ronen Zvulun
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.