Isa ga babban shafi
Iraq-Amurka

Bomb ya hallaka mutane 21 a Kirkuk ta Iraqi

Wani harin Bomb da aka kai a birnin Kirkuk na kasar Iraqi, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 21 wasu 118 kuma na can Rai a Hannun Allah

cbc.ca
Talla

Wata Majiyar Likitoci da jami’an tsaro ta tabbatar da cewar 2 daga cikin Boma-boman sun tarwatse ne kusa da wani Ginin jami’an tsaro wanda ba’a kammala ba, a yayin da na 3 kuma ya tarwatse a babbar Kofar shiga Kasuwa.

Harin dai ya zo ne a yayin da Dakarun kasar Iraqi da Kurdawa ke fafatawa da ‘yan tawaye masu tada kayar baya da suka fara kaddamar da hare-harensu a cinkin Watan Yunin wannan Shekarar inda suka mamaye akalla Larduna 5.

An ce dai Dakarun kasar Iraqin sun kaucewa yankin da suke rike da shi mai arzikin man Fetir a ardin Kirkuk.

Wannan kuma ya baiwa Kurdawa damar mamaye yankin da wasu yankuna na Arewacin kasar da suka dade suna kwadayin kai garesu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.