Isa ga babban shafi
MDD

Gaza: Kasashen Turai suna son a tsagaita wuta

Kasashen Faransa da Britaniya da Jamus sun yi kira ga Isra’ila da Hamas su gaggauta tsagaita wuta a cikin wani kudiri da suka gabatar a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin kawo karshen zubar da jinin da aka shafe makonni 6 ana yi a zirin Gaza.

'Yan uwan Mohammed Abou Shamala, daya daga cikin Shugabannin Hamas da Isra'ila ta kashe
'Yan uwan Mohammed Abou Shamala, daya daga cikin Shugabannin Hamas da Isra'ila ta kashe REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Wannan na zuwa ne bayan jiragen saman yakin kasar Isara’ila sun kai hare haren da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan kwamandojin kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

Ma’aikatan agaji a zirin Gaza sun tabbatar da mutuwar mutane hudu a wasu sabbin hare haren da Isra’ila ta kai a yau juma’a.

Yunkuriin kashen na Turai na zuwa ne a dai dai lokacin da rikicin na Gaza ke ci gaba da kazancewa, inda kuma yunkurin da kasar Masar ke jagoranta na kawo dukkan bangarorin biyu, kan teburin sasantawa, ke tabarbarewa.

Kasashen uku sun nemi a gaggauta samar da zaman lafiyan da zai kawo karshen harba makaman roka da hare haren soja a zirin gaza.

Masana harkokin diflomasiya sun ce kasashen na neman kulla yarjejeniya tsakanin membobin Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, kan wani kudurin samar da zaman lafiya.

A baya wasu kasashen da suka hada da Amurka, sun ki amincewa da wani kudurorin da kasar Jordan ta gabatar na neman Majalisar Dinkin Duniya ta sa baki a rikicin.

Zuwa yanzu sama da Falasdinawa 2,100 ne suka mutu, a rikicin da ya faro tun a ranar 8 ga watan Yulin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.