Isa ga babban shafi
Gaza

Masar ta yi kira ga Hamas da Isra’ila su koma teburin sulhu

Kasar Masar ta yi kira ga Isra’ila da Falasdinawa su koma teburin tattaunawa bayan sun yi fatali da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince. Masar ta da ta jagoranci tattaunawar a birnin Al Kahira ta bayyana takaicinta bayan bangarorin biyu sun kai wa juna hare hare.

Sojojin Isra'ila da makamansu a kusa da Gaza
Sojojin Isra'ila da makamansu a kusa da Gaza REUTERS/Baz Ratner
Talla

Kasar Masar tana kokarin ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta din din domin kawo karshen zubar da jini a Gaza.

Amma Kungiyar Hamas tace Isra’ila ta kashe iyalan daya daga cikin shugabanninta Mohammed Deif, yayin da bangarorin biyu suka koma musayar wuta kafin karewar yarjejeniyar da suka kulla ta sa’oi 24.

Bangarorin biyu sun zargi junansu da karya yarjejeniyar.

Israila tace ta kai hare hare sau 25 ba tare da yin cikakken bayani akai ba, yayin da Hamas ta yi ikrarin harba rokoki da dama zuwa Tel Aviv.

Ya zuwa yanzu dai an kashe Falasdinawa 2,026 a rikicin, yayin da Israila ta rasa mutane 67.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.