Isa ga babban shafi
Iraq

Mayakan ISIS sun sake tarwatsa wajen Ibadar ‘Yan shi’a

Mayakan ISIS da suka ayyana kafa daular musulunci a wani yanki na Iraqi sun sake tarwatsa wani waje da mabiya Shi’a ke ibada a birnin Mosul tare da tarwatsa wani kabari da aka ce na Annabi Shiyt ne Da ga Annabi Adam bayan sun tone wani Kabari da aka bayyana na Annabi Yunus ne.

Mutane sun taru a harabar Kabarin Annabi Yunus inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul
Mutane sun taru a harabar Kabarin Annabi Yunus inda Mayakan ISIS suka tarwatse a Mosul REUTERS/Stringer
Talla

Kamfanin Dillacin labaran Faransa ya ruwaito cewa mayakan sun tarwatsa wajen ibadar ne da bom a gaban idon mutanen birnin Mosul da suka karbe iko.

Wasu litattafai na tarihi na Addinin Musulunci da Kiristanci da Yahudanci sun ce Shiyt shi ne Da na uku ga Annabi Adam.

Amma mabiya Sunni suna nisanta kansu ga duk wandanda al’Qur’ani mi girma bai ambaci sunayensu ba domin gujewa Shirka.

Wannan dai na zuwa ne bayan Mayakan na ISIS sun tarwatsa wani waje da aka ce nan ne kabarin Annabi Yunus, bayan sun tarwatsa wurare da dama da mabiya shi’a ke ibada.

Rahotanni kuma sun ce Mayakan da suka ayyana kafa daular musulunci a Iraqi da Syria sun karbe ikon wani sansanin Sojin Syria a lardin Raga, tare da kashe sojoji da dama har ma da yi wa wasunsu yankan rago.

Adadin Sojoji akalla 85 ne kungiyar da ke sa ido ga rikicin Syria tace Mayakan na ISIS sun kashe a sansanin da Sojin da suka kwashe na Syria.

Daruruwan Sojoji ne aka ruwaito sun tsere zuwa wasu kauyuka da ke kusa da sansanin, amma kungiyar da ke sa idon tace akwai sojoji kimanin 200 da ba a san makomarsu ba.

Wani hoton Bidiyo da mayakan suka yada a kafar YouTube a Intanet, an nuna su a cikin sansanin Sojin suna kona hoton Shugaban Syria Bashar al Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.