Isa ga babban shafi
Iran-IAEA

Iran ta rage rumbun sanadarin uranium da kashi 75

Wani sabon rahoto da hukumar dake yaki da yaduwar makamin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA ta fitar a yau Alhamis, ya nuna cewa kasar Iran ta rage rumbun sanadarin uranium dinta da kashi 75.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani
Talla

Shi dai sanadarin uranium da shi ake amfani wajen samar da makamin nukiliya.

Iran ta aiwatar da wannan mataki a domin cika alkawarin da ta yi na rage uranium din a tsaiyar watan Aprilu.

A karkashin yarjejeniyar watan Nuwamba da aka yi, Iran ta yi alkawarin janye wani bangare na shirin samar da makamashin nukiliyanta ciki har da fanning bunkasa sanadarin na uranium.

Yin hakan zai ba da damar rage takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakabawa kasar.

A ranar 31 ga watan Mayu mai zuwa bangarorin biyu za su sake zama domin kulla yarjejeniya ta dindindin da za ta kawo karshen takaddamar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.