Isa ga babban shafi
Koriya ta Kudu

Ana ci gaba da aikin neman mutanen Koriya da suka nutse a teku

Ma’aikatan Agaji a kasar Koriya ta Kudu sun kwashe daren jiya suna ci gaba da neman mutane kusan 300 da suka bata daga hadarin jirgin ruwan kasar mai dauke da mutane 470 yawancinsu dalibai ‘Yan Makaranta.

Anna ci gaba da aikin ceto mutanen da jirgin ruwa ya kife da su a teku a kasar Koriya ta Kudu
Anna ci gaba da aikin ceto mutanen da jirgin ruwa ya kife da su a teku a kasar Koriya ta Kudu REUTERS/Hyung Min-woo/Yonhap
Talla

Bayanan farko sun yi nuni da cewa an yi nasara ceto mutane sama da 200 daga cikin 448 da hadarin ya rutsa da su a ruwan teku, galibinsu daliban makaranta, inda bayanan har ila yau suka tabbatar da mutuwar mutane hudu daga cikinsu.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar 9 daga cikin su, yayin da aka dinga anfani da fitula da kwale kwale cikin dare ko za’a yi nasarar samun masu sauran kwana.

Hukumomin sun ce suna ci gaba da neman sauran mutanen da ke cikin jirgin ruwan, kodayake hukumomin kasar sun bayyana fargaba akan makomar sauran fasinjojin da suka nutse a cikin tekun inda suka kara da cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu ya karu matuka.

Rahotanni na kuma nuna cewa rashin yanayi mai kyau na kawo cikas ga ci gaba da gudanar da ayyukan neman mutanen.

Akalla kwararrun a fannin ninkaya kusan 200 da wasu sojin ruwan kasar ke gudanar da ayyukan.

Bayanai daga hukumomi na nuna cewa a lokacin da hadarin ya auku, fasinja 448 ne a cikin jirgin da ya nutse a teku kusa da tsibirin Jeju, kuma cikinsu 324 dalibai ne da malamai 14 daga wata kamaranta a yankin Ansan da ke kudu da Seoul babban birnin kasar Koriya ta Kudu.

Suna kuma kan hanyarsu ne ta zuwa wani tsibiri inda za su je hutu. Babu wani bayani a hukumance da ya bayyana musabbabin aukuwar hadarin.

Firaministan kasar, Chung Hong-won ya bukaci ma’aikatan agajin da kar zu gaza har sai sun cim ma fasinjojin da suka bata, yayin da daya daga cikin ma’aikatan ke cewa da wuya a samu wani da ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.