Isa ga babban shafi
Syria

Syria: Assad yace suna samun nasara akan ‘Yan tawaye

Shugaban kasar Syria Bashar Assad yace Dakarunsa na samun nasara a yakin da ake fafatawa na tsawon shekaru uku inda aka rasa rayukan mutane akalla dubu dari da hamsin zuwa yanzu.

Shugaban kasar Syria  Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

Shugaba Assad da ke fuskantar matsin lamba daga kasashen yammaci da Larabawa ya yi wadannan ikirarin ne ta kafar kamfanin Dillancin labaran kasar na SANA.

Assad yace gwamnatinsa zata yi kokarin dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ‘Yan tawaye suka mamaye bayan dakarun shi sun yi kokarin karbe ikon wani sandanin ‘Yan tawaye a kusa da kan iyaka da Lebanon.

Akwai hare haren jiragen sama da dakarun Assad suka kai wa ‘Yan tawaye da Damascus, kamar yadda masu sa ido a rikicin kasar suka ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.