Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan gudun hijra sun jefi jerin gwanon motocin Brahimi

Rahotanni daga kasar Jordan na nuna cewa ‘Yan gudun hijirar kasar Syria a Jordan, sun yiwa jerin gwanon motocin mai shiga tsakani na Majalisar Dunkin Duniya, Lakhdar Brahimi, ruwan Duwatsu lokacin da ya bar sansanin ‘Yan gudun hijira dake Zaatari.  

Lakhdar Brahimi  sabon mai shiga tsakanin Rikicin kasar Syria
Lakhdar Brahimi sabon mai shiga tsakanin Rikicin kasar Syria DR
Talla

Kwakkwarar majiyar jami’an tsaro a sansanin na ‘Yan gudun Hijira, ta tabbatarwa wakilin Kamfanin Dillancin labarai na AFP cewa, akalla ‘Yan gudun hijira masu zanga-zanga 200 ne suka yiwo tsinke dauke da tarin Duwatsu a hannu, suna jifan jerin gwanon motocin mai shiga tsakani na majalisar dunkin Duniya, tareda yimasa kuwwa.

Cewa suke Fita! Fita! Brahimi yi gaba! Yi gaba can!!

A cewarsu sun fusata ne saboda ya gana da shugaba Bashar al- Assad, sannan yana kokarin bashi damar kara kisan jama’a.

Lakhdar Brahimi dai ya ce bisa dukkanin alamu inda aka tuma nan za’a cigaba da faduwa, saboda al’amarin sai kara tsananta ya ke, amma kuma yace yana iyakacin kokarinsa yaga ya taimakawa ‘Yan gudun hijirar su fita daga cikin yanayin da suke.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya dai sun nuna cewar fiyeda ‘yan gudun hijira 85, 197 ne aka yiwa rijista a Jordan, gashi kuma wasu 35, 961 na jiran tsammani.

Jami’ai a kasar ta Jordan sun ce, a Za’atari, kawai ‘Yan gudun hijira 30, 000, amma kuma duka-duka ‘yan gudun hijira 200, 000 ke akwai a yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.